Za a yi wa Marcos Alonso tiyata kan ciwon baya

Likitoci za su yi wa mai tsaron bayan Barcelona, Marco Alonso aiki, domin magance rashin buga wasa da yake sosai.

Dan wasan na fama da ciwon baya da yake hana shi sakat, tun da aka fara kakar bana.

Wasu hudu kacal Alonso ya buga a kakar nan, kuma uku daga ciki a sauyin dan wasa ya shiga.

Rabonda mai shekara 33 ya buga wa Barcelona wasa tun a Champions League a karawa da Shakhtar Donetsk ranar 7 ga watan Disamba.

Barcelona ba ta sanar da ranar da za a yi wa mai tsaron bayan aiki ba, sannan ba a fayyace ranar da zai koma buga tamaula ba koda an yi masa aikin.

Alonso ya koma Barcelona daga Chelsea a Satumbar 2022, bayan da ya yi kaka shida a kungiyar Stamford Bridge.

Lokacin da ya taka leda a Chelsea ya lashe Champions League da Premier League da kuma FA Cup.

Leave a comment