Za a yi gwanjon rigar Messi shida ta kofin duniya a Qatar

Za yi gwanjon rigunan tawagar Argentina da Lionel Messi ya saka a gasar kofin duniya a Qatar da kasar ta lashe a 2022.

Kyaftin Messi, mai shekara 36 ya daga kofin duniya, bayan da Argentina ta yi nasara a kan Faransa a bugun fenariti a Disambar bara a Qatar.

Har da rigar da ya sa a wasan karshe tana cikin wadanda za a yi gwanjonsu da ake cewar za ta kai fam miliyan takwas da wani kamfani Sotheby na New York zai gabatar.

Rigar da aka sayar mafi tsada a gwanjo a tarihi ita ce ta Diego Maradona kan fam miliyan 7.1 a 2022, rigar da ya ci Ingila kwallo da hannu kenan.

Gasar kofin duniya da aka yi a Qatar ita ce mafi kayatarwa da aka buga a tarihi, wadda kuma take da alaka da Messi dan kwallon Inter Miami.

Messi, mai Ballon d’Or takwas ya zama dan wasa na farko a kofin duniya da ya zura kwallo a raga a karawar cikin rukuni da ta tawagogi 16 da kwata fainals da wasan daf da karshe da na karshe a gasa daya.

Leave a comment