Za a karasa sayar da sauran tikikin kallon Euro 2024

Hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa ta sanar cewar ranar Alhamis za ta sayar da sauran tikitin kallon gasar cin kofin nahiyar Turai wato Euro 2024.

Za a sayar da sama da tikiti 100,000 na wasannin da dama ta hanyar intanet a kan yanar gizi-gizo a gasar da Germany za ta karbi bakunci.

Tun cikin watan Maris da Afirilu aka ci gaba da sayar da tikitin, inda aka tantance wadanda suka saya da kujerun da za a zauna a filayen da ta kai an fayyace karin gurin zaman ‘yan kallo da ta kai aka ci gaba da sayar da tikitin.

Kamar yadda Uefa ta sanar za a yi duba na tsanaki kan tikitin wurin zama na musamman.

Tun daga bara aka fara sayar da tikitin kallon Euro 2024 da tuni aka sayar da miliyan biyu da dubu dari bakwai.

Tawaga 24 za ta kara a Euro 2024 da za a fara daga 14 ga watan Juni zuwa 14 ga watan Yuli a German.

Leave a comment