Za a kafe alamar Olympic a Eiffel Tower a Paris

Mahukuntan wasannin Olympic sun sanar cewar za a kafe alamar gasar a Eiffel Tower a birnin Paris din France a shirin da ake na fara fafatawar bana.

Alamar da ta kunshi zobe biyar mai tsawon mita 15 da fadin mita 29, za a kafe ta a karshen Afirilu a Eiffel Tower da zai ke haskawa idan dare ya yi.

An sanar da hakan a shirin da ake na fatan kunna fitilar gasar ranar 16 ga watan Afirilu a Greece da hakan ke nufi kwana 100 kafin bude wasannin bana daga 26 ga watan Yuli zuwa 11 ga watan Agusta.

Ranar bikin budegasar kasashen da za su halarta za su ga wasu ‘yan wasa a wani kwale-kwale sun doshi Eiffel Tower daga Paris.

Lambobin yabon da za a lashe za su dauki alamar girmama Eiffel Tower wadda aka gina a 1889.

Leave a comment