Za a fara sayar da tikitin kallon gasar kofin Afirka a yanar gizo

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf za ta kaddama da fara sayar da tikitin kallon gasar kofin Afirka ta 2024 ta yanar gizo a karshe mako.

Wannan shi ne karon farko da hukumar za ta bayar da damar da magoya bayan tawagogi za su iya mallakar tikiti ta yanar gizo.

Za a fara sayar da tikitin daga ranar Asabar 11 ga wata Nuwambar 2023, ga wadanda suke da katin siyayya ta banki.

Kwana biyu tsakani wato ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba a sayar ga gama gari.

Za ka iya sayen tikitin ta nan http://tickets.cafonline.com/AFCON

Za a fara gasar cin kofin Afirka daga 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairun 2024 a Ivory Coast.

Za kuma a yi wasannin a filayen da ke Abidjan da Bouake da Korhogo da San Pedro da kuma Yamoussoukro.

Kudin tikitin zai kama daga 5000 FCFA kimanin dala takwas ta Amurka ajin mataki na uku.

Ajin mataki na biyu kuwa ya kama daga 10000 FCFA kimanin dala 16 ta Amurka, yayin da ajin farko za a sayar da tikitin kan 15000 FCFA kimanin dala 24 ta Amurka.

Leave a comment