Masu shigar da kara a Sifaniya na neman a daure Dani Alves shekara tara kamar yadda aka sanar ranar Alhamis.
Ana zargin tsohon dan kwallon Brazil da yiwa wata mata fyade a gidan rawa a Barcelona a cikin Disambar 2022.
Haha kuma masu shigar da karar na neman tsohon dan wasan Barcelona ya biya matar $163,500.
An tsare Alves cikin watan Janairun 2022 ba tare da an bayar da belinsa ba.
Dan wasan ya ce da amincewar matar suka yi mu’amula.
Tun cikin watan Agusta wata kotu a Barcelona ta tuhumi dan wasan, sannan ta ce tana da dukkan shaidun da za a tura shi gidan maza.
Yanzu dai ba a tsayar da ranar sauraren kakar Alaves ba, wanda ya buga wa Brazil gasar kofin duniya a Qatar a 2022.
Tun bayan da aka tsare dan wasan, kungiyarsa ta Mexico, UNAM ta soke kunshin kwantiragin da ke tsakaninsu.