Watakila a dakatar da Paul Pogba shekara hudu idan an sameshi da laifin shan abubuwan kara kuzarain wasa.
Hakan ya fito ne daga bakin ofishin masu shigar da kara a Italy.
An samu mai shekara 30 da laifin anfani da wani nau’in testosterone cikin watan Agusta, bayan wasan Serie A tsakanin Juventus da Udinese.
An tabbatar da samun dan wasan tawagar Faransa da laifi a samfurin jininsa da aka dauka, tun daga lokacin aka dakatar da shi a watan Satumba.
Kamar yadda wani rahoto ya ce a jaridar Gazzetta dello Sport, za a iya rage hukuncin daga shekara hudu zuwa biyu.
Dan wasan tawagar France ya buga wa kasarsa wasa 81 da lashe kofin duniya a 2018 a Rasha.
Ya sake komawa Juventus kan fara kakar bana daga Manchester United.
Tun farko ya fara taka leda leda a Bianconeri daga Manchester United tsakanin 2012-16.