Kawo yanzu kungiyoyi hudu ne suka ci wasa uku da suka buga a cikin rukuni a Champions League na bana.
Wadanda ake sa ran za su kai zagaye na biyu sun hada da Bayern Munich da Barcelona da Real Madrid da kuma mai rike da kofin Manchester City.
Haka kuma kungiyoyin suna daga cikin wadanda ake sa ran daya daga ciki za ta iya lashe kofin bana.
Duk wadda ta yi nasara a wasa na hur-hudu da za a buga ranar Talata da Laraba, za ta samu gurbin kai wa zagayen ‘yan 16 da za su ci gaba da wasannin.
Wasannin da za a buga Talata 7 ga watan Nuwamba
Dortmund da Newcastle
Shakhtar Donetsk da Barcelona
Atlético Madrid da Celtic
Lazio da Feyenoord
Milan da Paris St Germain
Man City da Young Boys
Crvena zvezda da Leipzig
Porto da Antwerp
Wasannin Laraba 8 ga watan Nuwamba
Napoli da Union Berlin
Real Sociedad da Benfica
Bayern da Galatasaray
Copenhagen da Man United
Arsenal da Sevilla
PSV Eindhoven da Lens
Real Madrid da Braga
Salzburg da Inter Milan