Za a ci gaba da Premier ranar Asabar

Za a ci gaba da Premier League ranar Asabar, bayan da aka kammala wasannin sada zumunta da na neman cike gurbin shiga Euro 2024 a makon da ya gabata.

An tsaya a wasa mako na 29 a gasar Premier League, bayan da wasu kungoyin keda kwantai daya wasu kuwa biyu ne a gabansu.

Arsenal mai wasa 28 tana ta daya da maki 64, iri daya da na Liverpool mai karawa 28 da tazarar maki daya tsakani da Manchester City mai fafatawa 28.

Aston Villa ce ta hudu gurbin karshe na shiga Champions League mai maki 56, wadda ta yi karawa 29.

Kungiyoyin da ke kasar teburi sun hada da Nottinghan Forest mai maki 21 ta 17 mai wasa 29, sai Burnley mai maki 17, wadda ta yi karawa 29 da kuma Sheffield United ta 20 mai wasa 28 mai maki 14.

Wasannin mako na 30 a Premier League

Ranar Asabar 30 ga watan Maris

  • Newcastle da West Ham
  • Bournemouth da Everton
  • Chelsea da Burnley
  • Nottm Forest da Crystal Palace (15:00)
  • Sheff Utd da Fulham
  • Tottenham da Luton
  • Aston Villa da Wolves
  • Brentford da Man Utd

Ranar Lahadi 31 ga watan Maris

  • Liverpool da Brighton
  • Man City da Arsenal

Leave a comment