Za a ci gaba da gasar Turkey cikin Disamba

Za a koma buga babbar gasar tamaula ta Turkiya ranar 19 ga watan Disamba.

An tsayar da wasannin bayan da shugaban kungiyar MKA Ankaragucu, Faruk Koca ya shiga fili ya naushi alkalin wasa, Halil Umut Meler.

Lamarin ya faru ranar Litinin a lokacin da aka tashi daga wasa a daya daga cikin wasan babbar gasar tamaula ta Turkey.

An sallami Meler daga asibiti a Ankara ranar Laraba, bayan da likitoci suka duba lafiyarsa, haka kuma ya amsa kiran shugaba, Recep Tayyip Erdogan ta wayar salula, wanda ya jajanta masa.

Shugaban hukumar kwallon kafar Turkey, Mehmet Buyukeksi ya ce ranar Alhamis za su sanar da hukuncin da suka dauka kan shugaba Faruk Koca.

Haka kuma za a sanar da ranakun da za a buga kwantan wasanni nan gaba.

Buyukeki ya kara da cewar rafli, Meler wanda ake mutuntawa a koda yaushe, mai shekara 37 mai busa wasannin gasar duniya, zai murmure domin yin alkalancin Euro 2024.

Tun farko ana cewa raflin zai yi ritaya da zarar ya murmure, domin ya tsira da rayuwarsa.

Jamus ce za ta karbi bakuncin wasannin gasar cin kofin nahiyar Turai tsakanin Yuni zuwa Yulin 2023.

Leave a comment