A karshen mako ake sa ran buga wasan hamayya tsakanin Kano Pillars da Barau FC a wasan mako na 29 a gasar Premier ta Najeriya.
Dukkan ƙungiyoyin suna buga wasansu a filin da ake kira Sani Abacha da ke Kofar Mata a jihar Kano, kuma a bana Barau ce ta yi nasara a kan Pillars a karawar da aka yi ba ƴan kallo.
Barau ɗin ta ci Pillars 2-1 a cikin watan Oktoba a lokacin da ƙungiyar da ake kira sai masu gida ta koma buga wasanni a Katsina, bayan hatsaniya a karawar da ta karɓi baƙuncin 3SC.
Wannan shi ne karo na biyu da za su fuskanci juna a gasar, bayan da Barau FC ta fara buga babbar gasar tamaula ta Najeriya a bana.
Pillars mai maki 32 tana ta 17 a kasan teburi, ita kuwa Barau FC tana ta 10 da maki 37.
Shin yaya kuke ganin wasan zai kaya – ku rubuta mana ra’ayinku.
