Za a buga kwantan wasan Bayern da Berlin cikin Janairu

Hukumar kwallon kafa ta Jamus ta sanar da za a buga kwantan wasan Bundesliga tsakanin Bayern Munich da Union Berlin ranar 24 ga watan Janairu.

Ranar Asabar da ta gabata ya kamata su kara a Allianz Arena, amma saukar dusar kankara ta hana wasan a Munich.

Dalilin da ya hana wasan saboda kare lafiyar ‘yan kallo, domin rashin kyawun yanayi ba zai bari a yi zirga-zirga ba, sannan ga cunkoson abubuwan hawa.

Bayern ta ce za a shiga wasan da tikitin da ‘yan kallo suka saya na wasan Asabar.

Wadanda ba za su samu damar zuwa karawar ba, sun kuma sayi tikitin za a sanar da ranar da za a mayar musu da kudinsu.

Saukar dusar kankara kan haifar da mugun cunkoson abin hawa a Kudancin Jamus, musamman da safe.

An dakatar da sauka da tashi a filin jirgin sama a Munich da tashar jirgin kasa, har da hana Jirga-jirga da daddare.

Leave a comment