Za a bayar da Yuro miliyan 8 ladan lashe Euro 2024

Duk tawagar da ta lashe gasar nahiyar Turai, Euro 2024, za ta karbi ladan Yuro miliyan takwas kamar yadda Uefa ta sanar ranar Asabar.

Wannan sanarwar ta fito a shirin da ake na gudanar da jadawalin wasannin da Jamus za ta karbi bakunci a 2024.

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta ce za ta bayar da ladan Yuro miliyan 331 a gasar ta badi – kamar yadda ta yi a Euro 2021.

Dukkan tawaga 24 da za ta buga wasannin za a bai wa kowacce kasa ladan Yuro miliyan 9.25 da kuma Yuro miliyan 1.5 ga duk wadanda za su kai zagaye na biyu kowacce.

Wadanda za su kai daf da na kusa da na karshe za su karbi Yuro miliyan 2.5, za kuma a bayar da Yuro miliyan hudu ga wadanda za su kai daf da karshe.

Haka kuma wadda ta yi ta biyu a gasar za ta karbi Yuro miliyan biyar.

Duk kasar da ta ci wasa za ta samu karin Yuro miliyan daya, idan aka yi canajaras kuwa ladan Yuro 500,000 za ta biya.

Kenan idan kasa ta lashe kofin nahiyar Turai na Euro 2024 tare da ladan wasannin da ta yi nasara zuwa daukar kofin za ta karbi Yuro miliyan 28.25

Leave a comment