‘Yan wasan Real Madrid da za su kara da Villareal

Real Madrid da Villareal za su buga wasan mako na 17 a La Liga a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.

Real Madrid tana ta biyun teburi mai maki 39, bayan da Girona ce ta daya da maki 41.

Villareal kuwa mai maki 16 tana ta 14 teburin La Liga, bayan wasa 16 kawo yanzu.

Wasa uku suka kara a bara a tsakaninsu, inda Villareal ta ci Real Madrid 2-1 a La Liga ranar 7 ga watan Janairun 2023.

A copa del Reay kuwa da suka kece raini ranar 19 ga watan Janairun 2023, Real Madrid ce ta yi nasara da cin 3-2.

Karawa ta uku a bara sun yi ne ranar 8 ga watan Afirilu a La Liga, inda Villareal ta ci 3-2 a antiago Bernabeu.

‘Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga​: Lunin, Kepa da Mario de Luis.

Masu tsaron baya: Alaba, Nacho, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Mendy da Tobias.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Valverde, Tchouameni, Ceballos da Nico Paz.

Masu cin kwallo: Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.

Wasannin mako na 17 da za a buga a La Liga ranar Lahadi:

  • Real Sociedad da Real Betis
  • UD Almeria da Real Marllorca
  • Las Palmers da Cadiz
  • Real Madrid da Villareal

Leave a comment