‘Yan wasan Real Madrid da suka je Alaves buga LaLiga

Real Madrid ta ziyarci Deportivo Alaves, domin buga wasan mako na 18 a La Liga ranar Alhamis a Mendizorroza.

Real Madrid ta doke Alaves gida da waje a bara, inda ta je ta ci Alaves 4-1 ranar 14 ga watan Agustan 2021,

Sannan ta dura 3-0 a Santiago Bernabawo ranar 19 ga watan Fabrairun 2022.

Tuni Carlo Ancelotti ya sanar da ‘yan wasan da Real Madrid ta je da su Alaves.

‘Yan wasan Real Madrid:

Masu tsare raga​: Lunin, Kepa da kuma Fran.

Masu tsare baya: Nacho, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Tobias da kuma Asencio.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Valverde, Tchouameni, Ceballos da kuma Nico Paz.

Masu cin kwallaye: Rodrygo, Joselu, Brahim da kuma Gonzalo.

Real Madrid tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki biyu tsakaninta da Girona ta daya mai maki 44.

Ita kuwa Alaves tana ta 14 a kasan teburi da makinta 16.

A jiyan Barcelona ta koma mataki na ukun teburi,, bayan da ta yi nasara a kan Almeria da ci 3-2.

Barcelona ta hada maki 38, Atletico ce ta hudu mai maki 35.

Wasannin da za a buga ranar Alhamis 21 ga watan Disamba:

  • Real Mallorca da Osasuna 
  • Real Betis da Girona   
  • Cadiz da Real Sociedad
  • Deportivo Alaves da Real Madrid

Leave a comment