‘Yan Tudun Wada United da za su kara da BIB FC

Tudun Wada United za ta ci gaba da buga Nationwide Davison One wasa na biyar a cikin rukuni ranar ranar Juma’a.

United, wadda ta lashe gasar ‘yan rukuni na biyu a bara za ta kece raini da BIB FC.

Kawo yanzu United ta ci wasa daya da canjaras biyu ta yi rashin nasara daya da maki biyar a shiyyar Daura, jihar Katsina, Nigeria.

Tun a ranar Laraba United ta tashi 1-1 da CP Boys a wasa na hudu a cikin rukuni, wadda ta fara cin kwallo daga baya aka farke.

Ranar Asabar da fara wasannin NLO 2024, United ta fara yin 1-1 da Mumbayya FC, sannan ta doke Famours Spiders 3-1 a karawa ta biyu cikin rukuni.

Daga baya ne United ta yi rashin nasara 3-1 a hannun Junior Danburan, wadda ake wasannin NLO a shiyyar Daura a filinta.

Tuni kociyan United, Anas Muhammad ya bayyana ‘yan wasa 11 da zai yi tata burza da BIB FC ranar Juma’a.

‘Yan Tudun Wada United da za su fuskanci BIB FC


1–muwadda muhd
2–Abdullahi Abububakar
3–Dickson ricky
4–Safiyanu Abdullahi
5–Najibullah musa
6–Salisu idiris
7–Jerry
8–musa yahaya
9–salisu Abdullahi
10–Aminu muhammad
11–Rabiu Abdullahi


Masu jiran ko-ta kwana

12–Sulaiman Haruna
13–Rabiu sani umar
14–Abdurahaman m ismail
15–Nasiru Hamza
16–Yusif muhammad
17–Nasiru Abdullahi
18–Nazifi muhd
19–Usman Garba
20–Tahir Adam L
21–Abdullahi y A
22–Rabilu Hamza
23-Ali Umar
24–Abdullahi Rabiu
25–Abdullahi Yau A

Sauran kungiyoyin da United za ta fuskanta nan gaba sun hada da Arewa FC da Ahzuba FC da kuma Katsina United.

Yadda teburi yake bayan wasan United hudu a cikin rukuni.

IMG 20240425 WA0010
IMG 20240425 WA0010

Leave a comment