‘Yan Real Madrid da za su kara da Man City a Champions League

Real Madrid za ta karbi bakuncin Manchester City a Santiago Bernabeu ranar Talata a zagayen kwata fainals a Champions League.

Tuni Real Madrid mai Champions League 14 ta sanar da ‘yan wasan da za su fuskanci Manchester City mai rike da kofin bara da ta lashe a karon farko a tarihi.

Wannan shi ne wasa na 10 da za su kara a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, inda kungiyar England ta yi nasara hudu ta Spain ta ci uku da canjaras uku.

Wasan da suka buga a bara a Champions League

Champions League Larabar 17 ga watan Mayun 2023

  • Man City 4 -0 Real Madrid

Champions League Talata 9 ga watan Mayun 2023

  • Real Madrid 1 – 1 Man City

A ranar ta Talata ake sa ran Carlo Ancelotti zai ja ragamar wasa na 200 a Champions League, wanda ya yi nasara 114 da lashe kofi hudu, biyu a AC Milan da kuma biyu a Real Madrid.

”Yan wasan Real Madrid:

Masu tsare raga: Lunin, Kepa da kuma Fran.

Masu tsare baya: Carvajal, Militão, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger da kuma Mendy.

Masu wasa daga tsakaiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Ceballos da kuma Arda Güler.

Masu cin kwallo: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.

Leave a comment