‘Yan Real Madrid da za su kara da Granada

Real Madrid za ta karbi bakuncin Granada ranar Asabar a wasan mako na 15 a LaLiga a Santiago Bernabeu.

Kungiyoyin biyu sun fafata a kakar 2021/22 inda Real ta je Granada ta ci 4-1 ranar 21 ga watan Nuwambar 2021.

A wasa na biyu ranar 6 ga watan Fabrairun 2022, Granada ta yi rashin nasara a hannun Real Madrid da ci 1-0.

Kawo yanzu Real tana matakin farko a teburin LaLiga da maki 35, iri daya da na Girona ta biyu.

Atletico mai kwantan wasa ce ta uku mai maki 31, iri daya da na Barcelona ta hudu.

Tuni dai Carlo Ancelotti ya sanar da ‘yan wasan da Real Madrid za su fuskanci Granada a gasar ta LaLiga.

‘Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Lunin, Kepa, Cañizares.

Masu tsare baya: Carvajal, Alaba, Nacho, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Mendy.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Valverde, Ceballos, Mario Martín, Nico Paz, Theo.

Masu cin kwallaye: Rodrygo, Joselu, Brahim, Gonzalo.

Leave a comment