‘Yan Barca da suka je PSG buga Champions League

Barcelona ta je Paris St Germain domin buga wasan farko a quater finals a Champions League da za su kara ranar Laraba a France.

Wannan shi ne karo na 14 da za su fuskanci juna a gasar zakarun Turai, inda Barcelona ta ci wasa biyar da canjaras hudu, PSG ta ci karawa hudu.

Wasan karshe da suka fuskanci juna a Champions League shi ne a 2020/21, Inda Barcelona ta yi nasara da cin 4-1 ranar Talata 16 ga watan Fabrairun 2021, sannan suka tashi 1-1 ranar Laraba 10 ga watan Maris din 2021 a France.

Barcelona ba ta yi wasa ba a karshen mako, bayan da aka yi karawar karshe a Copa del Rey, wanda Athletic Bilbao ta dauka, sakamakon cin Real Mallorca a bugun fenariti.

Tuni Xavi Hernandez ya sanar da ‘yan wasan da ya je da su France, domin buga wasan zagaye na daf da na kusa da na karshe, kafin su buga wasa na biyu ranar Talata a Estadi Olímpic Lluís Companys a Spain.

‘Yan wasan Barcelona da aka je da su France

Ter Stegen, ⁠João Cancelo, R. Araujo, I. Martinez, Ferran, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña, João Félix, Christensen, Fermín, Marcos A., Romeu, Vitor Roque, S. Roberto, Gündoğan, Kounde, Astralaga, Lamine Yamal, M. Casadó, Cubarsí, Marc Guiu da kuma H. Fort.

An kuma je PSG da Frenkie de Jong da Pedri, sai dai ba a fayyace ko suna da koshin lafiyar da za su buga wa Barca fafatawar, haka shima Gavi da shi aka je France.

Tsohon dan kwallon Barcelona, wanda ya yi mata koci a baya, Luis Enrique ne ke jan ragamar Paris St Germain, kenan wasan zai yi zafi domin ya san kungiyar Spain ciki da waje.

A kakar 2015 Enrique ya lashe kofi uku a Barcelona, mai shekara 53 ya yi kaka takwas a matakin dan wasa a Barca, sannan ya horar da kungiyar tsakanin 2014 zuwa

Haka shima Xavi tsohon dan kwallon Barca ne wanda ya lashe kofi sama da 20 a kungiyar, sannan ya ja ragamar daukar La Liga a bara a matakinsa na mai horar da kungiyar.

Xavi ya buga wa Barca wasa sama da 500, sannan ya yi ritaya a matakin koci a Nuwambar 2021, amma ya sanar zai yi ritaya a karshen kakar nan.

Barcelona mai Champions League biyar jimilla za ta buga zagayen quarter finals a karon farko a kaka hudu, yayin da PSG ba ta taba lashe kofin zakarun Turai ba.

Leave a comment