Ya za ta kaya tsakanin Wolves da Arsenal a Premier League?

Wolverhampton za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan mako na 34 a Premier League ranar Asabar a Molineux.

Arsenal ta doke Wolves 2-1 ranar Asabar 2 ga watan Disambar 2023, inda Bukayo Saka da Martin Odegaard suka ci mata kwallo, yayin da Matheus Cunha ya farke wa Wolves daya.

Arsenal tana ta biyu a teburin Premier League da maki 71 da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester City ta daya.

Ita kuwa Wolverhampton mai maki 43 tana ta 11 teburi, saura wasa shida ke gabanta.

Bayanai kan koshin lafiyar ‘yan wasan:

‘Yan wasan Wolves dake jinya sun hada da Matheus Cunha da Nelson Semedo da kuma Craig Dawnson.

Ana auna koshin lafiyar Rayan Ait-Nouri, haka kuma an sanar cewar Hwang Hee-chan ba zai buga wasa ba fiye da minti 45.

Ba wani dan wasan da ya ji sabon rauni a Arsenal, Jurrien Timber ne kadai ke jinya.

Bayanai kan haduwar kungiyoyin biyu

Arsenal na fatan cin Wolverhampton karo na shida a jere

Gunners ta zura kwallo a raga a kowanne wasa 32 da ta fuskabci juna a kowacce haduwa.

Kungiyar Wolverhampton Wanderers

Wolves wadda ba ta ci wasa hudu baya ba mai canjaras biyu aka doke ta biyu, ta yi nasara biyu da kungiyar da ke jan ragama a makon.

Ta yi rashin nasara uku a wasa gida daga biyar baya, wadda ta ci wasa tara aka doke ta hudu a Molineux.

Wasa daya ne ba ta zura kwallo ba a raga a fafatawa 26 a gida a dukkan karawa, shi ne a cikin Fabrairu da Brentford ta doke ta 2-0.

Wolves ce kadai daga manyan gasar Turai biyar ba ta ci kwallo ba daga wajen da’ira ta 18 a kakar nan.

Kungiyar Arsenal

Arsenal na fatan buga wasa na shida a jere a waje ba tare da an zura mata kwallo ba a raga a karon farko a tarihi – wadda take rike da wannan bajintar ita ce Liverpool a kakar 2014/15.

Gunners ta yi nasarar cin wasa daga 17 da ta fuskanci kungiyar da ke kan mataki na 10 zuwa karshen teburi, wadda ta yada maki a hannun Fulham da canjaras daya aka doke ta katawa daya.

Saura kwallo biyu take bukata daga 37 da ta ci a waje ta yi kan-kan-kan da wanda ta taba yi a Premier League a 2010/11.

Bukayo Saka yana da hannu a cin kwallo takwas a wasa bakwai a waje da zura bakwai ya bayar da daya aka zura a raga.

Leave a comment