Ya kamata Juventus ta koma buga Champions League

Massimiliano Allegri ya ce ya kamata Juventus take buga Champions League, bayan da za ta kara da Salernitana ranar Lahadi a gasar Serie A ta Italy.

Juventus za ta samu gurbin shiga gasar badi, idan har ta samu maki uku ranar Lahadi, wadda a baya aka dakatar saboda karya UEFA da ta shafi cinikayyar ‘yan kwallo daidai samu da ake kira Financial Fair Play.

Kungiyar da Allegri ke jan ragama, wadda za ta buga Coppa Italia da Rome ranar Laraba, ana ganin ita ce za ta lashe karawar ranar Lahadi, bayan da Salernitana ta fadi daga gasar bana za ta koma buga mai daraja ta biyu a Italy.

Bayan da ta kasa cin wasa biyar baya, Allegri ya ce wannan kakar ta jawo kalubale kasancewar ba su buga Champions League ba.

Ya kara da cewar ya kamata Juventus ta koma ana damawa da ita a Champions League, domin hakan yana da mahimmaci ga kungiyar da kwallon Italy.

Juventus na auna koshin lafiyar, Kenan Yildiz da Federico Chiesa domin buga wasan na ranar Lahadi, yayin da Alex Sandro da Danilo da De Sciglio ke jinya, watakila sai karawa da Atalanta su koma taka leda.

Leave a comment