Xavi zai ci gaba da horar da Barcelona zuwa karshen 2025

Xavi ya amince zai ci gaba da jan ragamar Barcelona zuwa karshen kakar 2025, bayan da ya canja shawara.

A cikin wata Janairu tsohon dan kwallon Barcelona, mai shekara 44 ya sanar cewar zai ajiye aikin jan ragamar kungiyar a karshen kakar nan.

Yanzu dai Xavi wanda ya dauki La Liga a bara ya amince zai ci gaba da horar da Barcelona, bayan da shugaban Barcelona, Joan Laporta ya sanar da shi amfanin ci gaba da jan ragamar kungiyar.

Xavi ya karbi aikin horar da Barcelona cikin Nuwambar 2021, bayan barin Al Sadd ta Qatar, wanda ya ja ragamar kungiyar Camp Nou ta dauki La Liga a kakar 2022/23.

Sai dai kungiyar tana ta biyu a kan teburin gasar bana da tazarar maki 11 tsakaninta da Real Madrid mai jan ragama.

Barcelona ta yi ban kwana da Champions League na kakar nan, bayan da Paris St Germain ta fitar da ita.

Xavi, wanda ya dauki kofi 25 a lokacin da ya buga wa Barcelona tamaula, ya sanar zai ajiye aikin, bayan rashin nasara a hannun Villareal da cewar ba a kare muradunsa a kungiyar Camp Nou.

Sai dai tun daga lokacin da ya sanar zai ajiye aikin, sai abubuwa suka sauya a Barcelona, wadda ta yi wasa 10 a jere ba a doke ta, daga baya ta yi rashin nasara a hannun Real Madrid 3-2 a El Clasico a La Liga ranar Lahadi.

Ranar Laraba aka yi aka yi taro a gidan Laporta, inda aka rarrashi Xavi da ya ci gaba da horar da Barcelona.

Idan kociyan ya kara inganta wasan kungiyar a badi kakar 2024/25, lallai kungiyar na aiki da wanda ya kara darajar kungiyar.

Leave a comment