Women World Cup 2027: USA da Mexico za su karbi bakunci

Amurka da Mexico sun mika bukatar hadakar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata da za a yi a 2027.

Ana sa ran kasashen biyu za su fuskanci adawa daga Brazil da wasu daga nahiyar Turai da za su iya nuna bukatarsu ciki har

Belgium da Germany da kuma Netherlands.

Idan kasashen Kudancin Amurkan suka yi nasara, za su samu karin manyan gasar tamaula ta duniya da za su gudanar.

Amurka ce za ta karbi bakuncin wasannin Copa America a shekara mai zuwa da kuma Fifa Club World Cup a 2025.

Haka kuma za a gudanar da gasar cin kofin duniya na maza a 2026 a Amurka da Canada da Mexico.

An gudanar da gasar cin kofin duniya ta mata a bana a Australia da New Zealand, inda Spain ta lashe, bayan cin England 1-0 a wasan karshe.

Amurka ta gudanar da gasar cin kofin duniya ta mata karo biyu a 1999 da kuma 2003.

Gasar karshe ta kofin duniyar mata da aka gudanar a Arewacin Amurka tun 2015 da Canada ta shirya wasannin.

Amurka ce kan gaba a yawan lashe gasar cin kofin duniya ta mata mai hudu jimilla.

Leave a comment