Watakila za a soke VAR a Premier League a badi

Kungiyoyin Premier za su kada kuri’a ko ya dace a soke amfani da VAR daga kaka mai zuwa a taron da za su gudanar a watan gobe.

Wolverhampton ce ta fata miki wannan bukatar daga baya sauran kungiyoyi 19 da suke buga gasar suka bukaci a kada kuri’a a taron da za a yi a Harrogate ranar 6 ga watan Yuni.

Kungiyoyin sun ce an kirkiri VAR da kyakkyawan fatan domin yin adalci, amma sai batun ya koma rashin tabbas, sai a zura kwallon da bai kamata ba, sai a bayar da hakuri, sannan a sake aikata laifin.

An fara aiki da VAR a 2019, domin taimakawa alkalin dake cikin fili gudanar da aiki ko yanke hukuncin takaddama cikin adalci, amma kuma an yi ta samu korafe-korafe kan yadda ake amfani da na’urar.

  • Barcelona za ta kara da Almeria domin ci gaba da zama ta biyun teburi

Ana bukatar kungiyoyi 14 daga 20 su amince a soke VAR kafin a amince da daina amfani da fasahar daga kaka ta bana.

Tuni dai kungiyoyin Premier League suka zabi a fara amfani da na’urar da za take tantance satar gida daga kaka ta 2024-25.

Leave a comment