Watakila Varane ya bar Man United a karshen kakar nan

Wasu rahotanni na cewar watakila mai tsaron bayan Manchester United, Rafael Varane ya bar kungiyar a karshen kakar nan.

Tsohon dan wasan tawagar Faransa, ya koma Old Trafford da taka leda daga Real Madrid a 2021.

Ya buga wa United wasa 75 da cin kwalo biyu, ya bayar da daya aka zura a raga, tun bayan da ya koma kungiyar.

Varane yana da sauran kunshin yarjejeniyar da za ta kara da United zuwa karshen Yunin 2025

Wasu kungiyoyi da dama daga Saudi Arabia na son daukar dan wasan a watan Janairu, idan an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ta Turai.

Haka kuma wasu rahotannin na cewar zai iya komawa Bayern Munich, domin buga Bundesliga.

To sai dai kuma da kyar ne idan United za ta bar mai tsaron bayan ya bar Old Trafford a Janairu, wadda take fama da masu jinya da yawa.

Leave a comment