Watakila Tuchel ya maye gurbin Ten Hag a Man United

Kociyan Bayern Munich, Thomas Tuchel yana sawun gaba cikin wadanda ake cewar zai maye gurbin mai horar da Manchester United, Erik ten Hag.. (Football Insider)

Thomas Partey da Jesus suna daga cikin ‘yan wasan da kungiyoyin Saudi Arabia ke fatan bai wa kwantiragi mai tsoka, domin daukar ‘yan kwallon Arsenal. (Express)

Ana tantama kan makomar Callum Wilson a Newcastle, wanda ake cewar zai bar St James Park a karshen kakar nan. (Mirror)

Borussia Dortmund na fatan rike Jadon Sancho zuwa kakar badi, amma da kyar idan Manchester United za ta sayar da dan kwallon, wanda ke wasannin aro, ya kuma koma kan ganiyai. (Sky Sport Germany)

Dan wasan Stuttgart, Serhou Guirassy yana daga cikin wanda mai horar da Arsenal, Mikel Arteta zai dauka idan an kammala kakar nan, domin ya kara karfin gurbin masu cin kwallaye. (Fichajes – in Spanish)

Fatan da Kalvin Phillips ke yi na komawa Leeds United ya dogara idan kungiyar Elland Road ta samu gurbin shiga Premier League. (Football Insider)

AC Milan na shirin sayen Jonathan David daga Lille da zarar an kammala kakar nan. (Calciomercato – in Italian)

Leave a comment