Watakila Haaland ya sake zama gwarzon Premier a bana

Watakila dan wasan Manchester City, Erling Haaland ya lashe kyautar gwarzon Premier League na bana, kuma na biyu a jere.

An kara zabar dan kwallon mai shekara 23, domin sake takara a bana har da takwaransa na City, Phil Foden.

Sauran da suke cikin takarar gwarzon Premier na kakar nan sun hada da dan wasan Arsenal, Martin Odegaard da Declan Rice da na Chelsea, Cole Palmer da na Newcastle, Alexander Isak da na Aston Villa, Ollie Watkins da na Liverpool Virgil van Dijk.

Za a kada kuri’ar tsakanin alumma, yayin da jami’an Premier League za su sanar da zakara ranar 18 ga watan Mayu.

Haka kuma za a sanar da gwarzon koci da ake takara tsakanin Pep Guardiola, wanda ya lashe kyautar karo hudu a baya da na Arsenal, Mikel Arteta da na Liverpool, Jurgen Klopp da na Villa, Unai Emery da kuma na Bournemouth, Andoni Iraola.

A bara ne Haaland ya lashe kyautar da ta matashin dan wasa mafi hazaka, bayan cin kwallo 36 a wasa 35 a lik.

Kawo yanzu ya zura 25 a raga a City, shi ne kan gaba a wannan bajintar a bana.

Tsohon dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo shi ne wanda ya taba lashe kyautar karo biyu a jere a 2006-07 da kuma 2007-08.

Gwarzon dan wasan Premier League na bana

  • Erling Haaland (Man City)
  • Phil Foden (Man City)
  • Declan Rice (Arsenal)
  • Martin Odegaard (Arsenal)
  • Alexander Isak (Newcastle)
  • Ollie Watkins (Aston Villa)
  • Cole Palmer (Chelsea)
  • Virgil van Dijk (Liverpool)

Kociyoyin dake takarar gwarzon Premier League na kakar nan

  • Pep Guardiola (Man City)
  • Mikel Arteta (Arsenal)
  • Jurgen Klopp (Liverpool)
  • Unai Emery (Aston Villa)
  • Andoni Iraola (Bournemouth)

Masu takarar matashin dan wasan Premier League na bana

  • Erling Haaland (Man City)
  • Phil Foden (Man City)
  • Bukayo Saka (Arsenal)
  • William Saliba (Arsenal)
  • Alexander Isak (Newcastle)
  • Cole Palmer (Chelsea)
  • Kobbie Mainoo (Man Utd)
  • Destiny Udogie (Tottenham)

Leave a comment