Watakila Galatasaray ta ɗauki matakin shari’a kan Liverpool

Galatasaray ba ta ji daɗi ba kan raunin da Noa Lang ya ji a wasa da Liverpool a Champions League ranar Laraba.

Ɗan wasan ya ji rauni ne, bayan karo da allon talla na gefen filin Afield a karawar da Liverpool ta yi nasara.

Liverpool ta kai kwata fainal bayan cin Galatasaray 4-0, kenan 4-1 gida da waje.

Raunin da Lang ya ji sai ɗaukarsa aka yi a kan gadon marasa lafiya daga baya aka yi masa tiyata.

Haka kuma ɗan ƙwallon ya sanar a kafarsa ta sada zumunta cewar an yi masa aiki cikin nasara yana murmurewa.

Wasu rahotanni daga Turkiya na cewa Galatasaray ta shigar da korafi ga hukumar ƙwallon kafa ta Turai, UEFA kan lamarin.

Da wannan sakamakon Liverpool za ta kara da Paris St Germain gida da waje a zagayen kwata fainal.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top