Watakila Ederson ya gama buga wa Man City wasa a bana

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya ce yana fargaba ko Ederson ya gama tsare ragar kungiyar a bana, bayan raunin da ya ji ranar Lahadi.

Dan kwallon tawagar Brazil an sauya shi a karawar da City ta doke Nottingham Forest 2-0 ranar Lahadi, sakamakon ciwo da yake ji a allon kafada a gasar mako na 35.

Golan ya ji raunin ne a karon da ya yi da dan wasan Forest, Willy Boly, daga nan ne likitoci suka duba lafiyarsa.

Mai shekara 30 ya ci gaba da tsare ragar City zuwa karshen zagayen farko, daga nan aka sauya shi da Stefan Ortega.

City ta ci kwallo ta hannun Josko Gvardiol da kuma Erling Haaland, wanda ya zura na biyu a raga, kuma na 21 a kakar bana, saura wasa hudu a gaban kungiyar Etihad.

Bayan da City ta yi nasara ranar Lahadi ya sa ta koma ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki daya tsakani da Arsenal, wadda take jan ragama.

Leave a comment