Real Madrid ta sanar Thibaut Courtois ya ji rauni a wasan Champions League da Manchester City ranar Talata.
City ta karɓi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu a gasar zakarun Turai a Etihad, inda ta yi rashin nasara 2-1.
Kenan Real Madrid ta kai zagayen kwata fainal da cin 5-1 gida da waje, za ta fuskanci Bayern Munich a wasan gaba.
A karawar ce golan Real Madrid, Courtois ya ji raunin da aka canja shi da Andriy Lunin.
Tuni dai ake hasashen cewar mai tsaron ragar ɗan kasar Belgium, zai yi jinyar mako shida.
Idan kuwa har hakan ta tabbata, kenan ba zai buga wa Real wasan hamayya da Atletico Madrid ranar Asabar ba.
Haka kuma ba zai yi wasan Champions League gida da waje da Bayern Munich ba.
Ana kuma cewa da ƙyar ne idan zai fuskanci Real Mallorca da Girona da Alaves da kuma Real Betis a La Liga.
Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da maki huɗu tsakani da Barcelona ta ɗaya, ita kuwa Atletico tana ta uku da tazarar maki tara tsakaninta da Real Madrid