Vinicius ba zai buga wa Real Madrid wasa da Napoli ba

Real Madrid ta bayyana ‘yan wasan da za su kara da Napoli a Champions League ranar Laraba, wasa na bibyar-biyar a cikin rukuni.

A cikin watan Oktoba, Real Madrid ta je Italiya ta doke Napoli da ci 3-2 a wasa na bibiyu a cikin rukuni na uku.

Bellingham, wanda ya ci kwallo na uku a wasa da Cadiz a La Liga ranar Lahadi, zai buga wasan, bayan jinya da ya yi.

To sai dai Vinicius Junior ba zai buga karawar ba tare da Aurelien Tchouameni da Luca Modric.

A rukuni na uku, Real ce ta daya da maki 12, sai Napoli mai maki bakwai ta biyu da Sporting Braga mai uku da kuma Union Berling mai maki daya.

Real Madrid mai kofin 14 na Champions League na bukatar maki daya daga wasa biyun da suka rage a rukuni na uku.

‘Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Lunin, Fran da kuma Cañizares.
Masu tsare baya: Carvajal, Alaba, Nacho, Lucas V., Fran García, Rüdiger da kuma Mendy.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Valverde, Ceballos, Mario Martín, Nico Paz da kuma Theo.
Masu cin kwallaye: Rodrygo, Joselu, Brahim da kuma Gonzalo.

Wasannin da za a buga ranar Laraba:

  • Sevilla da PSV Eindhoven        
  • Galatasaray da Manchester United        
  • Arsenal da Lens
  • Real Madrid da Napoli    
  • Real Sociedad  da Red Bull Salzburg       
  • Bayern Munich da FC Kobenhavn  
  • Sporting Braga         da Union Berlin      
  • Benfica da Inter Milan

Leave a comment