Villareal za ta dauki Pellistri daga Manchester United

Villareal na son daukar dan kwallon Manchester United, Facundo Pellistri.

Mai shekara 22 yana buga wa Man United wasa a bana, wanda ya yi karawa 13 a dukkan fafatawa, amma bai ci kwallo ba ya bayar da daya aka zura a raga.

Pellistri ya koma Old Trafford daga Penarol a 2020, wanda ya buga karawa 23 har da 13 a bana kawo yanzu a Man United.

Dan kwallon tawagar Uruguay yana da kunshin yarjejeniya da Manchester United zuwa karshen kakar 2025.

Wasu rahotanni na cewar Erik ten Hag yafi son amfani da Amad Diallo, saboda haka Pellistri zai amince ya bar Old Trafford a Janairun nan.

An kuma ce Man United a shirye take ta saurari tayi mai tsoka daga wasu kungiyoyin, amma tana son bayar da aron dan kwallon maimakon sayar da shi.

Pellistri ya shiga wasa sauyi a karawa da West Ham United a Premier League ranar 23 ga watan Disamba.

Tun daga nan bai yi mata wasa ba da ta fafata da Aston Villa da kuma Nottingham Forest ba.

Dan kwallon ya taka leda a wasannin aro a Alaves a kakar 2020-21 da kuma a 2021-22.

Pellistri ya buga karawa 35 a Alaves a kaka biyun da ya yi ba tare da cin kwallo ba, wanda ya bayar da daya aka zura a raga.

Leave a comment