Victoria ba zai karbi bakuncin Commonwealth games 2026 ba

Masu shirya Commonwealth Games sun sanar cewar suna neman kasar da za ta karbi bakuncin wasannin 2026, bayan da Australia ta janye a cikin watan Yuli.

Gasar ta ci karo da koma baya, sakamakon da birnin Victoria ya ce shirya wasannin da dan karen tsada ba zai iya ba.

Kimanin sama da ‘yan wasa 4,000 daga mambobi 54 na Commonwealth ne ke shiga wasannin.

A wani taro da ta gudanar a Singapore, mahukuntan gasar sun sanar cewar suna ta kokarin neman wadda za ta maye gurbin Australia, domin shirya wasannin 2026.

A lokacin babban taron an kara Gabon da Togo a cikin mambobin kasashen da ke buga Commonwealth Games.

Kasashen biyu daga Afirka, wadanda Faransa ta rena sun mika bukatar shiga wasannin da ake gudanarwa duk bayan shekara hudu.

Canada ma ta janye daga goyon bayan birnin Alberda, domin karbar bakuncin karawar 2030, mako daya da Victoria ta sanar da hakura da shirya fafatawar 2026.

……………..

Leave a comment