Verstappen ya lashe Las Vegas Grand Fri

Mai rike da kofin gasar tseren motocin Formula 1 ta bana, Max Verstappen ya lashe Las Vegas Grand Prix ranar Lahadi.

Charles Leclerc matukin motar Ferrari, shi ne na biyu, wanda ya zarta Ferrari Sergio Perez na Red Bull daf da za a karkare tseren

Verstappen ya fara da jan ragamar tseren tn farko, wanda aka hukunta dakika biyar bayan aikata laifi.

Leclerc ya yi kokarin wuce karbar jan ragama a zango na 17, yayin da Verstappen ya je canja taya, wanda ya yi dakikar da aka yanke masa.

Leave a comment