USYK NA FATAN DAMBATAWA DA FURY CIKIN FABRAIRU

Oleksandr Usyk na fatan dambensa da Tyson Fury ajin babban nauyi da ya kamata a yi shi cikin watan Fabrairu a Saudi Arabia.

Tun farko an tsara za su kara a tsakaninsu ranar 23 ga watan Disamba, amma mai shirya dambe Frank Warren ya fada a makon jiya cewa da kyar ne idan hakan zai yiwu.

A watan jiya Fury ya yi nasara a kan Francis Ngannou a Saudi Arabia a damben da ta kai da takaddama.

A makon gobe za a tsayar da ranar da Usyk da Fury za su dambata a wasan da ake kishirwar kallo.

Leave a comment