Uruguay ta gayyaci Suarez domin ya fuskanci messi

Uruguay ta kira Luis Suarez domin ya buga mata wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za ta kara da Argentina a makon nan.

Suarez, wanda shi ne kan gaba a ciwa kasarsa kwallaye a tarihi mai 68 na kan ganiya a gasar Brazil a Gremio mai 16 a raga a wasa 29 a bana,

karon farko da Marcelo Bielsa ya gayyace shi tun bayan da ya karbi aiki a watan Mayu.

Edinson Cavani, wanda ya ci kasar kwallo 58 ba zai yi karawar ba, bayan da ya ji rauni a kungiyarsa ta  Boca Juniors.

Argentina wadda kawo yanzu ta ci wasa hudu a cikin rukuni tana ta daya da maki 12 da tazarar byar tsakaninta da Venezuela da Brazil da kuma Uruguay.

Tawaga shida ce daga Kudancin Amurka za ta je gasar cin kofin duniya da za a buga a Canada da Mexico da Amurka a 2026.

Leave a comment