Dan wasan Liverpool, Darwin Nunuz ya ci kwallo biyu a wasan da Uruguay ta ci Bolivia 3-0 a neman shiga gasar kofin duniya.
Da wannan sakamakon Uruguay tana ta biyu a teburin Kudancin Amurka da tazarar maki biyu tsakaninta da Argentina ta daya.
Colombia ta ci gaba da sa kwazo, bayan da ta ci Paraguay 1-0 a Asuncion, ita kuwa Chile rashin nasara ta yi da ci 1-0 Quito a hannun Ecuador.
Colombia, wadda ba ta buga gasar kofin duniya ba a Qatar a 2022 tana ta ukun teburi da maki 12.
Chile kuwa tana ta takwas a kan teburi da maki biyar, Peru kuwa da Venezuela tashi suka yi 1-1 da Lima.
Za a dauki ‘yan shidan farko a teburin Kudancin Amurka zuwa gasar kofin duniya da za a yi a Amurka da Canada da Mexico a 2026.
Yayin da wadda take ta bakwai za ta je wasannin cike gurbi.