Urawa za ta kara da Man City a Fifa Club World Cup

Mai rike da kofin zakarun Asia, Urawa Red Diomonds ta doke Club Leon 1-0 a Fifa Club World Cup ranar Juma’a a Saudi Arabia.

Dan kasar Netherlands, Alex Schalk ne ya ci kwallon a minti na 78, wanda ya shiga karawar daga baya.

Da wannan sakamakon kungiyar Japan za ta fuskanci Manchester City ranar Talata a zagayen daf da karshe

Sai a ranar Asabar Man City za ta ziyarci Saudi Arabia, bayan ta tashi a karawa da Crystal Palace a gasar Premier League a Etihad.

Manchester City mai rike da kofin zakarun Turai a bara, ta lashe Premier League da kuma FA Cup a karon farko a tarihi.

Ita kuwa kungiyar Brazil, Fluminense mai rike da Copa Libertadores ta kai zagayen daf da karshe kai tsaye, bayan da ta dauko hutu.

Kenan za ta jira wadda za ta kai zagayen gaba a wasan da za a buga ranar Juma’a tsakanin mai rike da kofin zakarun Afirka, Al Ahly da Al-Ittad, mai kofin babbar gasar Saudi Arabia.

Leave a comment