Union Berlin da Bjelica sun raba gari a tsakaninsu

Union Berlin ta kori kociyanta Nenad Bjelica ranar Litinin duk da cewar shugaban kungiyar yana goyon bayansa.

Union ta yi rashin nasara 4-3 da wadda take kasan teburi Bochum ranar Lahadi, wadda take mataki daya daya tsakani daga ‘yan karshen teburi, bayan wasa biyu a karkare kakar bana.

Cikin watan Nuwamba Bjelica ya karbi aiki horar da Berlin, bayan da ta kori Urs Fischer, sakamakon rashin sakamako masu kyau, wanda ya kai kungiyar Champions League a bara.

Kungiyar ta sanar cewar Marco Grote da mataimaki Marie-Louise Eta, za su yi aikin rikon kwarya wasa biyu da ya rage har da na ranar Asabar da Cologne, wadda itama ke fuskantar barin Bundesliga.

Leave a comment