Undav ne gwarzon Bundesliga a Nuwamba

Dan kwallon Stuttgart, Deniz Undav shi ne aka zaba fitatcen dan wasan Bundesliga na watan Nuwamba.

Ya yi takara a zaben da ‘yan kallo ke kada kuriya tare da dan wasan Bayern Munich, Harry Kane da Leroy Sane da na Bayer Leverkusen, Alex Grimaldo da kuma na RB Leipzig, Xavi Simons.

Undav ya buga wa Stuttgart dukkan wasa uku a Bundesliga a cikin Nuwamba da cin kwallo uku, Harry Kane ne ke gabansa mai shida da Alejandro Grimaldo mai hudu.

Ba dan wasan da ya kai shi kai hare-hare guda 10, shi ne na biyu a yawan kirkirar damar cin kwallo sau hudu.

Wadanda ke gabansa a buga kwallo ya nufi raga sau 14, Harry Kane da Leroy Sané da Xavi Simons da kuma Loïs Openda.

Leave a comment