Tudun Wada United za ta kara da Katsina Junior ranar Lahadi

Kungiyar kwallon kafa ta Tudun wada United za ta fuskanci Katsina Junior a wasa na shida a cikin rukuni a NLO National League Division One shiyyar Daura a jihar Katsina.

Tudun Wada United wadda ta yi wasa biyar a rukunin tana da maki takwas, bayan cin wasa biyu da canjaras biyu aka doke ta karawa daya tana ta biyun teburri.

Ita kuwa Katsina Junior mai maki bakwai tana ta hudu teburi, bayan da ta yi nasara biyu da canjaras daya, sannan aka doke ta biyu daga ciki.

Junior Danburan ce ta daya a kan teburi mai wasa shida da maki 15, wadda ta yi nasara biyar aka doke ta wasa daya tal.

Tun kafin wasan Tudun Wada United za a fara fafatawa tsakanin Arewa FC da Ahzuba FC da sanyin safiyar Lahadi.

NLO 2024 Tudun Wada United Daura Katsina
Tudun Wada United Table

Bayan an antashi wasan Tudun Wada United ne za a yi tata burza tsakanin Famours Spiders da BIB daga nan Junior Danburan ta kara da CP Boys da yammaci.

Leave a comment