Tudun Wada United za ta fafata da Famous Spiders a Daura

Tudun Wada United za ta kara da Famous Spiders a wasa na biyu a cikin rukuni a Nigerian Nations Wide League rukunin farko.

United, wadda ta tashi 1-1 a wasan farko da Mumbayya FC a daura jihar Katsina, za ta kara ne da sanyin safiyar Litinin.

Tun kan nan za a fara fafatawa tsakanin Azuba FC da Mumbayya, sauran karawar cikin rukunin ranar Litinin har da wasa tsakanin Junior Danburan FC da Arewa FC da wanda CP Boys za ta kara da Katsina United.

Tuni kociyan Tudun Wada United Anas, ya bayyana ‘yan wasan da za su kara da Famous Spiders:

‘Yan wasan Tudun Wada United:

1–Muwdda Muhamad
2- -Abdullahi Abubakar
3–Abdullahi yau A
4–Nasiru Hamza
5– Najibullah musa
6–Salisu idiris
7–Jerry Okon
8–Nasiru Abdullahi
9–Salisu Abdullahi A
10–Aminu muhd
11–Rabiu Abdullahi

Masu jiran ko-ta-kwana

12–Sulaiman Haruna
13-Rabiu sani umar
14–Abubakar m ismail
15–Nasiru umar A
16–Yusif muhd
17–musa yahaya
18–Safiyanu Abdullahi
19–Nazifi muhd
20—ibrahim dauda
21–Usman garba
22–Tahir Adam L
23–Ali Umar
24–Rabilu Hamza
25–Abdullahi Rabiu

Leave a comment