Tudun Wada United za ta fafata da Bib a NLO 2024

Tudun Wada United za ta buga wasa na biyar a cikin rukuni da Bib a Nationwide League Division 1 ranar Alhamis.

Ranar Laraba Tudun Wada United ta tashi 1-1 da CP Boys a wasa na hudu a cikin rukunin da take wasa a Daura a jihar Katsina, Nigeria.

CP Boys ce ta daya a rukunin daura mai maki bakwai a wasa uku, Sai Junior Danburan ta biyu da maki shida, bayan karawa uku, sai Ahzuba ta uku da maki biyar bayan wasa uku, sannan Tudun Wada United ta hudu da maki biyar a wasa hudu.

Ranar Litinin Tudun Wada ta yi rashin nasara a hannun Junior Danburan da cin 3-1, kafin nan United ta doke Famours Spiders 3-1, bayan da ta tashi 1-1 da Mumbayya FC ranar Asabar.

Tudun Wada mai rike da National League two na fatan kai wa zagayen gaba a wannan rukunin da ake wasa a gidan Junior Danburan a Daura, jihar Katsina, Nigeria.

Leave a comment