Tudun Wada United za ta buga Nation Wide a Katsina

Kungiyar kwallon kafa ta Tudun Wada United za ta buga Nation Wide League a Daura a jihar Katsina, Nigeria, bayan an kammala shagulgulan bikin karamar Sallah.

Kungiyoyi takwas ne za su kece raini a tsakaninsu a rukunin da yake na 14 da aka raba, domin su buga wasannin kakar bana 2024/25.

Cikin kungiyoyin da suke rukunin sun hada da biyu daga jihar Katsina mai masaukin baki da kuma shida daga jihar Kano har da Tudun Waa United a cikinsu.

Kungiyoyi biyu daga Katsina sun hada da Katsina Junior FC da kuma Junior Danburan.

Sauran shida daga jihar Kano kuwa sun hada da Arewa Pillars da Famous Spiders da Tudun Wada United da Sky Academy da Mumbayya da kuma Barau.

Tuni dai kungiyoyin suka shiga yi wa ‘yan wasa rijistar, wadanda za su buga Nations Wide League na bana da za a buga a wurare 16.

Wuraren sun hada da Jihar Lagos da wanda za a yi a filin wasa na Remo Stars da na Maracana da wasu kuma dai a filin wasa na Remo Stars dukkan su a jihar Lagos, Nigeria.

Akwai wani rukuni a Osun da Osogbo da Ilorin da Akure a filaye biyu da Ibadan da Calabar da Umuahia da Oisa da Omoku da Delta da Lafia da Bwari da Area 3 da Bauchi da Gombe da Kebbi da Daura da Kaduna da Kontagora da Jigawa har wuri biyu.

Duk kungiyar da ta lashe kofin bana, za ta karbi mota mai cin mutum 18 da kudinta ya kai naira miliyan 30.

Leave a comment