Tudun Wada ta yi rashin nasara a hannun Junior Danburan

Tudun Wada United ta yi rashin nasara 3-1 a hannun Junior Danburan a wasa na uku a cikin rukuni a Nationswide division One ranar Talata.

Ana fara wasa Junior Danburan ta ci kwallo ta hannun Jamilu Yusuf nod daga tamaula da ya Salmanu ya buga masa, daga baya Tudun Wada ta farke ta hannun Salisu Abdullahi a minti na 23 a wasan da suka buga a Daura a jihar Katsina..

Sai dai kuma Junior Danburan ta zura na biyu a raga, bayan da dan wasan Tudun Wada, Salisu Abdullahi ya ci gida, kuma haka suka je hutun rabin lokaci, Junior Danburan tana da cin 2-1.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Tudun Wada ta yi ta kokarin farke kwallon, amma hakan bai samu ba, inda Junior Danburan ta samu damar cin na uku saura minti shida a tashi ta hannun Shamsu Kabir.

Da wannan sakamakon Tudun Wada United ta ci wasa daya da canjaras daya an doke ta daya da maki hudu, bayan karawa uku.

Ta fara 1-1 da Mumbayya FC, sannan ta ci Famours Spiders 3-1, yayin da ta yi rashin nasara 3-1 a hannun Junior Danburan.

Za a ci gaba da wasanni na hudu a cikin rukuni ranar Laraba, inda Tudun Wada United za ta fafata da CP Boys FC, ita kuwa Junior Danburan da ake buga gasar bana a gidanta, za ta fuskanci Mumbayya FC.

Kawo yanzu Junior FC tana ta daya a kan teburi da maki shida, wadda ta ci wasa biyu da rashin nasara daya, sai CP Boys ta biyu mai wasa biyu da nasara biyu mai maki shida, BIB FC maki hudu ne da ita mai karawa biyu da kuma Tudun Wada United mai maki hudu, bayan karawa uku.

Leave a comment