Trippier ba zai buga wasan Ingila da Arewacin Macedonia ba

Kieran Trippier ya hakura da wasan da Ingila za ta buga da Arewacin Macedonia ranar Litinin.

Hukumar kwallon kafar Ingila ta sanar cewar mai tsaron bayan mai shekara 33 ba zai yi wasan karshe a cikin rukuni a neman shiga Euro 2024 ba.

Ta ce tuni dan kwallon ya koma gida, bayan da zai je ya magance wata matsala ta kashin kansa.

Tuni kuma Newcastle United ta sanar cewar Tripper ya koma gida, bayan da ya baro sansanin Ingila da Gareth Southgate ke jan ragama.

Tun a baya Ingila ta samu gurbin shiga gasar da Jamus za ta karbi bakunci a 2024, bayan da take jan ragamar rukuni na uku.

Ta doke Malta 2-0 ranar Juma’a, kuma Trippie ya buga karawar, inda Ingila ta hada maki 19 daga wasa bakwai.

Wasan gaba da Newcastle United za ta buga shi ne da Chelsea ranar 25 ga watan Nuwamba.

Leave a comment