Trabzonspor za ta buga wasa shida ba ‘yan kallo

An umarci Trabzonspor ta buga wasa shida ba ‘yan kallo, bayan rikicin da ya barke a makon jiya a gasar Turkiya da Fenerbahce ta yi nasara.

Magoya baya da yawa ne suka shiga fili suka farma ‘yan wasan Fenerbahce da jami’an tsaro a karawar da aka yi a Papara Park a Trabzon.

An dakatar da dan wasan Fenerbahce Jayden Oosterwolde da Irfan Can Egribayat daga buga wasa daya, bayan da suka yi fada da wasu magoya bayan Trabzonspor.

An kuma ci tarar Trabzonspor Lira miliyan uku, kwatankwacin (£75,000).

An dakatar da kocin Trabzonspor, Egemen Korkmaz, daga jan ragamar wasa daya, bayan da aka same shi da laifin yin fada da bakin.

Ba a hukuntan dan wasan Nigeria ba, Bright Osayi-Samuel, wanda aka gan shi kwance a kasa, bayan da magoya baya suka shiga filin wasan.

An yanke wannan hukuncin ne, bayan kammala taron da kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon kafar Turkiya ya gabatar.

Ranar Talata mambobin Fernabahce suka kada kuri’ar kin fice wa daga gasar kwallon kafar Turkiya, sakamakon yawan tashin hankali a lokacin tamaula.

Rikicin da ya faru a Trabzonespor ya faru ne a minti na 87 lokacin da Michy Batshuayi ya ci kwallo daga nan magoya baya suka fara jifa cikin fili.

Shugaban hukumar kwallon kafar duniya, Gianni Infantino ya ce ba za a amince da lamarin ba.

Fenerbahce tana ta biyu a teburin Super Lig, bayan wasa 30 da tazarar maki biyu tsakani da mai jan ragama Galatasaray.

Leave a comment