Thompson ta raba gari da kociyanta Osbourne

Mai rike da lambar yabo biyar ta zinare a Olympic, Elaine Thompson-Herah ta raba gari da kocinta, Shanikie Osbourne.

Hakan ya biyo bayan shirin da take na kare matakinta a gasar Olympic da za a yi a birnin Paris a 2024.

Thompson-Herah ta raba gari da kociya, Osbourne, bayan da ta ce karin albashin da ya bukata ya wuce kima da tunani.

Ta ce kocin ya bukaci karin albashi da kudi mai tsoka, sannan ba wata hanyar da za su zauna domin kamo bakin zaren, shi ya sa ta hakura da shi.

Thompson-Herah, mai shekara 31, ita ce ta biyu a tseren mita 100 a Eugene din Amurka a Oregon a 2021, wadda ta kare a sakwan 10 da dkika 54.

Wadda take da tarihin a duniya ita ce Florence Griffith-Joyner a gasar Olympic a 1988 Olympic.

Thompson-Herah ta mamaye guje-gyje tsawon lokaci, wadda ta lashe mita 100 da 200 a Rio din Brazil da kuma a Tokyo Olympic da kuma tseren mita 400 na ‘yan wasa hudu a Tokyo.

Sai dai ‘yar wasan ta yi fama da jinya a 2023 da hakan ya sa ta kasa samun gurbin shiga gasar duniya da aka yi a Budapest cikin Agusta.

Leave a comment