The IOC ya amince Russia da Belarus su shiga Olympic 2024

Kwamitin Olympic na duniya ya amince ‘yan wasan Russia da na Belarus su shiga gasar Olympic a 2024, amma a matakin masu cin gashin kai.

The IOC ya ce shiga wasannin zai zama a kan ka’ida, sai kuma ‘yan wasa sun cika dokokin da aka gindaya.

Kwamitin ya yanke wannan matsayar tun bayan da ake ta kiraye-kiraye kan makomar Russia da Belarus a wasannin da birnin Paris zai shirya a 2024.

Cikin dokokin da aka gindaya ‘yan wasan Russia da na Belarus za su shiga wasannin a karkashin tutar Olympic.

Hakan na nufin ba za a rera taken kasar Russia da Belarus ba a Paris, sannan ba wata alamar tutar kasashen idan za su yi wasa.

Leave a comment