Ten Hag ya ce har yanzu kofa a bude take ga Sancho

Erik ten Hag ya ce Jadon Sancho ya san abinda ya kamata ya yi, idan har yana son ceto sana’arsa ta tamaula daga lalacewa.

Sancho, wanda United ta saya £73 million daga Borussia Dortmund a 2021, baya bugawa babbar kungiyar tamaula tun bayan sabani tsakaninsa da Ten Hag cikin Satumba.

Dan wasan England, an sanar da shi ya koma atisaye shi kadai, bayan da ya rubuta sako a kafarsa ta sada zumunta da cewar kociyan na son dora alhalin rashin kwazon kungiyar a kansa.

Watakila a raba gari tsakanin dan wasan da United a watan Janairu, amma kuma za ta yi hasara babba kan dan kwallon da take biyu £350,000 a duk mako.

To sai dai Ten Hag ya ce har yanzu kofa a bude take ga dan wasan mai shekara 23, idan har yana son ci gaba da taka leda a kungiyar.

Sancho ya ci kwallo 12 a wasa 82 a Man United, amma rashin dan wasan ya bai wa Alejandro Garnacho damar yin wasa sosai a kungiyar.

United ta yi amfani da Garnacho maimakon Marcus Rashford a ranar Laraba a wasan da ta doke Chelsea 2-1 a Premier League.

Leave a comment